大象传媒

Wydad ta lashe kofin zakarun Afirka

  • Published
alamar nasarImage source, Getty Images
Image caption,

Nasara

Klub din Wydad Casablanca ya lashe klub din Alahly na kasar Masar da ci biyu da daya.

Wannan kuma shi ne karo na biyu a cikin tarihi, da klub din na Wydad Casablanca na Morocco ke yin nasarar samun kasancewa zakaren-zakarun Afirka.

A dai ranar Asabar ne, Kungiyar kwollon kafa ta Wydad Casablanca ta Morocco, ta kuduri amfani da shiga gaban da ta yi tun da farko a birnin Alexandria.

Ta yi nasara da ci daya da nema .

Haka kuma duk da martanin da Al ahly ke kaimata, klub Alahly ya kasance wanda ya cin kofin har sau 8.

Kuma ya kasance shi ne kan gaba a gida, wato a fadin kasar ta Masar a dukan tsawon shekara a fagen tamola .

Yan wasar klub din na Alahaly sun kuma dauki dukan matakan da suka dace domin tsare baya.

To sai dai 'yan wasa na Wydad Casablanca suka gano su .

Image source, Getty Images
Image caption,

Klub din ya lashe ALhaly ta Masar da ci biyu da daya a wasan da suka yi.

A cikin mintoci 69 suka saka kwollo daya domin su tabbatar da nasarar su ,kwallon da Achraf Ben Charki ya harbo da kuma Walid El Karty suka tura a cikin raga.

Wannan ya baiwa Wydad ci 2 da 1 kuma 'yan wasan suka kai ga cikkakiyar nasara.

Bayan wannan matsayi da klub din ya samu, ya kuma samu kyauta ta kudi dala miliyan 2.5.

Haka zalika kungiyar ta Wydad Casablanca ta Morocco, za ta wakilci nahiyar Afirka a wata mai zuwa a gasar cin kofin duniya na klub-klub a Hadaddiyar daular larabawa.

Wannnan nasara ga 'yan kwallon kasar Morocco ta kasance gida biyu. Babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar, za ta halarci wata karawa a kasar Cote-D'ivoire a mako mai zuwa.

Kuma nasarar kungiyar ta Atlas Lions ko kuma les lions de l'Atlas, za ta ba ta damar halartar gasar cin kofin duniya ta shekara mai zuwa a kasar Rasha.